Ballewar annobar kyandar biri: Yadda zaku kare kan ku daga kamuwa da kwayar cutar

Ballewar annobar kyandar biri: Yadda zaku kare kan ku daga kamuwa da kwayar cutar

- An samu ballewar annobar kyandar biri a Yenagowa ta jihar Bayelsa

- Tun shekarar 1970 rabon da a samu rahoton kamuwa da cutar a Najeriya

- Dabbobin da suka fi yada wannan kwayar cuta sune; bera, kurege, da kuma jaki

- Duk da ana iya warkewa bayan kamuwa da cutar, bincike ya nuna babu wani takamaiman maganin ta

An samu ballewar annobar kyandar biri a Yenagowa ta jihar Bayelsa, inda yanzu kimanin mutum 11, cikinsu harda wani likita, ke kawwame a asibiti karkashin kulawar likitoci da kuma gudanar da bincike.

Ita dai wannan cuta ba kasafai ake kamuwa da ita ba domin tun shekarar 1970 rabon da a samu rahoton kamuwa da cutar a Najeriya. Cutar ta samo asali ne daga dabbobi kuma tana iya yaduwa daga mutum zuwa mutum. Dabbobin da suka fi yada wannan kwayar cuta sune; beraye, kurege, da kuma jaki.

Ballewar annobar kyandar biri: Yadda zaku kare kan ku daga kamuwa da kwayar cutar

Ballewar annobar kyandar biri: Yadda zaku kare kan ku daga kamuwa da kwayar cutar

Duk da ana iya warkewa bayan kamuwa da cutar, bincike ya nuna babu wani takamaiman maganin wannan cuta, domin ko a lokaci na karshe da cutar ta bulla a Najeriya saida tayi sanadiyar mutuwar mutum 10.

DUBA WANNAN: Kotu ta sa Hukumar Soji su biya diyyar miliyan N85 saboda kisan farar hula

Hukumar hana yaduwar cuta ta kasa ta bayyana hanyoyin da za a bi domin kare kai daga kamuwa da wannan muguwar cuta. Hanyoyin sune kamar haka; gujewa kusantar dabbobin da suka fi yada wannan cuta kamar yadda muka lissafa su a sama, wanke hannu da sabulu bayan taba dabba, yayin duba dabba maras lafiya a sanya safar hannu, ma'aikatan lafiya su kara taka tsan-tsan wajen duba marasa lafiya sannan su kara ankarewa da duk maras lafiya da ya zo asibiti domin nazarin alamomin cutar kyandar biri tare da gaggauta mika labarin kamuwa da cutar zuwa babbar cibiyar lafiya mafi kusa.

Babban darektan hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa, Chikwe Ihekweazu, yayi kira ga jami'an lafiya dasu cigaba da duba masu dauke da cutar ba tare da jin tsoro ba, matukar dai sun zamo masu kiyaye dokokin kare kai yayin duba masu dauke da cutar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel