Kotu ta sa Hukumar Soji su biya diyyar miliyan N85 saboda kisan farar hula

Kotu ta sa Hukumar Soji su biya diyyar miliyan N85 saboda kisan farar hula

- Shekaru 8 kenan da sojin suka kashe Olajide Olinari

- A watan Yanairun 2009 ne Soji suka raunata mamacin a Apapa da ke Legas, ya kuma rasu bayan gajeruwar jinya

- Garin fulawa yake sayarwa a lokacin yana raye

Access to Justice, wata kungiya ta masu kare hakkin danAdam, ita ta kai kara kan kisan gilla da sojin Najeriya suka yi wa Olajide, bayan da suka far masa a kan hanyarsa ta zuwa gida daga kasuwa, a watan daya na shekarar 2009.

Kotu ta sa Hukumar Soji su biya diyyar N85 saboda kisan farar hula

Kotu ta sa Hukumar Soji su biya diyyar N85 saboda kisan farar hula

A wancan lokaci, yana gaban gingimarinsa a Apapa ta jihar Legas, sojin suka far musu shi da direbansa, inda suka yi masa dukan kawo wuka da belet dinsu, wanda ya farfasa masa kai, raunuka da suka sa ya rasa ransa yayin jinya.

A karar da kungiyar ta shigar, ta sanya sunan shugaban hukumar sojin na wancan lokacin, da sauran kusoshin hafsoshin sojin kan lallai sai an yi adalci kan irin zaqewar da soji keyi wajen muzgunawa farar hula.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji fadar Aso Rock

Yanzu dai kotu a jihar Legas din ta sami sojin da laifi, inda kuma ta bada odar a biya iyalansa diyyar naira miliyan tamanin da biyar.

Ko hakan na nufin wasu ma da ke da irin wannan korafi zasu iya zuwa kotu domi neman adalci?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel