Rikita-Rikita: Ma'aikatan man fetur na shirin shiga wani gagarumin yajin aiki

Rikita-Rikita: Ma'aikatan man fetur na shirin shiga wani gagarumin yajin aiki

Ya zuwa yanzu dai labarin da muke samu daga majiyoyi da dama na nuni ne da cewa ma'aikatan hukumar dake kula da albarkatun man fetur da iskar gas ta kasa na nan suna kishin-kishin din fara yajin aikin sai baba ta gani a dukkan fadin kasar.

Mun samu dai cewa ma'aikatan na hukumar dake kula da albarkatun man fetur da iskar gas din sun ce za su shiga yajin aikin ne nan ba da dadewa ba bisa zargin da suke yi wa gwamnatin tarayya da kin biyan su hakkokan su da suke bi a kwanan baya.

Rikita-Rikita: Ma'aikatan man fetur na shirin shiga wani gagarumin yajin aiki

Rikita-Rikita: Ma'aikatan man fetur na shirin shiga wani gagarumin yajin aiki

KU KARANTA: APC bata cancanci zama jam'iyya ba

NAIJ.com dai ta samu cewa ma'aikatan na hukumar dake kula da albarkatun man fetur da iskar gas sun bayyana cewa yanzu haka dai suna bin gwamnatin tarayya makudan kudaden da suka tasar wa Naira biliyan 800.

Idan ba'a manta ba kasar dai na fama da matsalolin rashin kudi da kuma rikice-kiricen kwadago inda a kwanan baya ma ma'aikatan lafiya da kuma malaman jami'oi suka shiga yajin aiki suma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel