Jami'an yan sandan jihar Kaduna sun cafke gaggan barayin mutane 11 da suka addabi jihar

Jami'an yan sandan jihar Kaduna sun cafke gaggan barayin mutane 11 da suka addabi jihar

Jami'an rundunar yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kaduna a jiya Laraba 4 ga watan Oktoba sun gabatar da wasu gaggan barayin mutane da kuma masu fashi da makamin da suka addabi jihar dama makwaftan ta ga yan jarida.

Jami'an yan sandan dai sun gabatar da wadannan bata garin ne a farfajiyar hedikwatar hukumar dake Jere na jihar ta Kaduna kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na rundunar ya bayyana.

Jami'an yan sandan jihar Kaduna sun cafke gaggan barayin mutane 11 da suka addabi jihar

Jami'an yan sandan jihar Kaduna sun cafke gaggan barayin mutane 11 da suka addabi jihar

KU KARANTA: Hanyoyin anfani 9 na bawan ayaba

NAIJ.com dai ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar CSP Jimoh Moshood ya bayyana cewa gaggan masu laifin dai da suka kama sune suka dade suna addabar jama'a a hanyoyin Birnin Gwari - Funtua da Birnin Gwari zuwa Kaduna da Abuja zuwa Kaduna da ma Kaduna zuwa Kano.

Haka ma dai jami'in ya shaidawa manema labaran da suka halarci hedikwatar cewa muggan makaman da suka kama daga hannun su sun hada da bindigogi 3 da harsasai 72 da kuma bindigar gargajiya kwara 3 da sauran wasu kayan tsafe tsafe na su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel