Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

- Dalibi ya sha guba domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarraba

- Ya yanke shawarar kashe kansa ne bayan da hukumar makarantar ta bayyana cewar bai tsallake daya daga cikin jarrabawar da ya sake rubutawa ba

- Binciken ya nuna cewar yanzu haka an sallami dalibin daga asibiti

Wani dalibin makarantar faltaknik dake Lafiya a jihar Nasarawa, yayi yunkurin hallaka kansa bayan da ya kwankwadi madarar fiya-fiya saboda faduwa jarrabawar daya daga cikin darussan karatun sa.

Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Jaridar Punch ta rawaito cewar dalibin, Chinedu Iromuanya, ya yanke shawarar kashe kan sa ne bayan da hukumar makarantar ta bayyana cewar bai tsallake daya daga cikin jarrabawar da ya sake rubutawa ba a shekarar 2016.

Binciken jaridar ta Punch ya nuna cewar yanzu haka an sallami dalibin, dan asalin Jihar Abiya, daga asibitin Dalhatu dake garin Lafiya ranar talata, kamar yadda ma'aikaciyar asibitin da bata yadda a bayyana sunanta na ta tabbatar.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

Bincike ya nuna cewar har yanzu hukumar makarantar faltaknik din bata sanar da 'yan sanda faruwar al'amarin ba, kuma koda aka tuntubi shugaban makarantar, Dakta Silas Gyar, ya ce bazai yi magana da manema labarai ba.

Hakazalika hukumar 'yansanda a jihar ta Nasarawa ta bakin kakakinta na hulda da jama'a, DSP Idrisu Kennedy, ta ce bata da labarin faruwar lamarin domin hukumar makarantar bata sanar da su ba, amma sunyi alkawarin yin bincike domin tabbatar da dalilin da yasa dalibin daukar wannan mataki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel