Gwamnatin jihar Ebonyi zata baiwa tsagerun IPOB Naira 250,000 ko wanen su

Gwamnatin jihar Ebonyi zata baiwa tsagerun IPOB Naira 250,000 ko wanen su

Gwamnatin ihar Ebonyi da ke a kudu maso gabashin kasar nan ta fara tattara rajistar sunayen tsagerun kungiyar nan ta IPOB na jihar domin ta koya masu sana’o’i tare da kuma basu jarin dogaro da kai.

Kwamishinan inganta tattalin arzikin jihar ne dai ya sanar da hakan mai suna Uchenna Orji ga manema labarai jiya Laraba a Abakaliki babban birnin jihar.

Gwamnatin jihar Ebonyi zata baiwa tsagerun IPOB da Naira 250,000 ko wanen su

Gwamnatin jihar Ebonyi zata baiwa tsagerun IPOB da Naira 250,000 ko wanen su

KU KARANTA: Yadda wani matashi a Zamfara ke kera injin sarrafa shinkafa

NAIJ.com ta samu kuma dai cewa jami'in gwamnatin ya kuma ce wadannan matasa na jihar, dadin baki ne kawai akayi musu aka rude su suka shiga kungiyar ta 'yan aware na Biafra.

Haka ma dai Kwamishinan Mista Uchenna Orji ya ce ana cigaba da aikin yi musu rajistar ne a kananan hukumomin jihar 13 sannan kuma ya kara da cewa za a samar wa matasa 12,000 aiki ta hanyar raba musu naira 250,000 kowane domin ya kama sana’ar dogaro da kan sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel