Gwamnatin Kano za ta samar da ingantaccen irin tumatir da sunadarai na miliyan 250

Gwamnatin Kano za ta samar da ingantaccen irin tumatir da sunadarai na miliyan 250

- Gwamnatin jihar Kano za ta samar da ingantaccen irin tumatir da sunadarai na kudi naira miliyan 250

- Za a rarraba irin tumatir ga manomar tumatir da kwayar cutar ta shafa kimanin shekaru biyu da suka shude

- Gwamnatin jihar Kano tare da haɗin gwiwar Bankin Aikin Noma za su ba da tallafin na naira biliyan 2 ga manoma a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta amince dakudi naira miliyan 250 domin samar da ingantaccen irin tumatir da sunadarai don rarrabawa ga manomar tumatir wadanda wata cutar tumatir ta shafa a fadin jihar.

Farfesa Mahmoud Daneji, babban daraktan hukumar noma da raya karkara a jihar (KNARDA), ya bayyana wannan a wani taron masu ruwa da tsaki wanda aka sani da YieldWise Nigeria Stakeholders a Kano a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

Shirin YieldWise wanda Gidauniyar Rockefeller ke tallafa wa ta hanyar haɗin gwiwar PYXERA Global tare da manufar rage yawan asarar bayan girbi.

Gwamnatin Kano za ta samar da ingantaccen irin tumatir da sunadarai na miliyan 250

Gwamnan jihar Kano, Umaru Ganduje

Yace da zarar an samo tsaba da sunadarai, za a rarraba su ga masu nomar tumatir da kwayar cutar da ke cinye gonaki ta shafa kimanin shekaru biyu da suka shude.

KU KARANTA: Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar, tare da haɗin gwiwar Bankin Aikin Noma (BoA), sun shirya shirin bayar da kuɗi naira biliyan 2 ga manoma a jihar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Daneji ya ce wani ɓangare na wannan tallafi za a ba manomar tumatir a kokarin bunkasa samar da tumatir da kuma karfafa mutane da dama don su rungumi sana’ar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel