'Yan majalisa 2 na wakilai sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

'Yan majalisa 2 na wakilai sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

Wasu 'yan majalisar wakilai biyu, Zephaniah Jisalo da Yusuf Tijjani sun sauya shekar jam'iyya daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai ci a yanzu.

Majalisar ta tabbatar da sauyin shekar wannan wakilan na ta yayin da shugaban majalisar Yakubu Dogara yake karanta rubutanttun wasikun su a zaman na majalisa.

Jisalo mai wakiltar mazabar Bwari dake birnin tarayya da kuma Tijjani mai wakiltar mazabun Okene/Ogori-Magogo dake jihar Kogi, sun bayyana wannan sauyin sheka ne a wasiku daban-daban da suka rubutawa majalisar.

'Yan majalisa 2 na wakilai sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

'Yan majalisa 2 na wakilai sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

A yayin mayar da martani, shugaban wakilai maras rinjaye na majalisar Umar Barde, ya hikaito daga sashe na 68 na kundin tsarin kasa da yake nuna cewa duk wani dan majalisa da sauya shekar jam'iyya zai sauka daga kujerar sa ne. Shi kuwa shugaban majalisar Dogara ya bayyana cewa, kotu ce kadai za ta iya zartar da wannan hukunci.

KARANTA KUMA: Wata sabuwar cuta makamaciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda

Naij.com ta fahimci cewa tun a farkon shekarar nan, akwai 'yan majalisar guda uku da suka yi sauyin sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, wadanda suka hadar da; Edward Pwajok na jihar Filato, Hassan Saleh na jihar Benue da kuma Adamu Kamale na jihar Adamawa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel