Kotu ta daure wani magidanci da matarsa da ta kama da laifin aikata fyade ga ‘yar aikin su

Kotu ta daure wani magidanci da matarsa da ta kama da laifin aikata fyade ga ‘yar aikin su

- Wata kotu ta gurfanar da ma’aurata biyu a jihar Lagas

- An gurfanar da mata da mijin ne bisa zargin aikata fyade da kuma cin zarafin mai yi musu aiki

- Kotu ta ba da belin ma'auratan akan kudi naira 400,000

Wata kotun dake zaune a yankin Surulere a jihar Legas ta yi ram da wasu ma’aurata biyu bisa zargin fyade da cin zarafin yar aikinsu mai shekaru 10.

Mai karan Anthonia Osayande ta bayyana wa kotu cewa mijin mai suna Onubogu mai shekaru 54 a duniya yayi wa mai aikin tasu fyade ta karfin tuwo cikin dare a watan Afirilu yayinda ita kuma matar Gloria mai shekara 45 ta fara matsawa yarinyar tun daga watan Afirilu zuwa watan Satumba sanadiyyar fyaden da mijin ya yi.

Ta kara da cewa mai aikin ta ji rauni sanadiyyar duka da fyade da ma’auratan suka yi mata sannan kuma suka ki kaita asibiti domin a duba lafiyar ta.

Kotu ta daure wani magidanci da matarsa da ta kama da laifin aikata fyade ga ‘yar aikin su

Kotu ta daure wani magidanci da matarsa da ta kama da laifin aikata fyade ga ‘yar aikin su

Ma’auratan sun ki amincewa da zargin da aka yi musu sannan alkalin kotun A. Ipaye-Nwachukwu ta bada bellin su akan Naira 400,000.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta kama jami’ai 2 dake saida bindigogi ga yan fashi da masu satar mutane

Sharudun belin da alkain ta bada ya hada da kowanen su ya kawo takardun shaidan biyan haraji wa gwamantin jihar Legas guda biyu.

Alkalin ta bada umurin kai yarinyar asibiti domin ta sami kulan da take bukata sannan ta daga sauraron karan zuwa 11 ga watan Nuwamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel