CBN ta karyata kamun mataimakin gwamnan ta

CBN ta karyata kamun mataimakin gwamnan ta

Babban Bankin Najeriya (CBN) ta musanta labari dake cewa hukumar EFCC ta kame daya daga cikin darektocin ta.

Mista Isaac Okorafor, mukaddashin daraktan bayanai na CBN, ya fadi haka ne a Abuja a ranar Laraba cewa rahoton bai da tushe.

“An jawo hankalin CBN kan rahoto dake zargin kamun daya daga cikin mataimakan daraktan ta wanda ya kai ga asarar wasu kudade zuwa ga hukumar EFCC.

“Muna son mu bayyana bisa wasu sharruda cewa babu alamar gaskiya cikin abinda rahotan ke fadi, kuma ba tare da shakka ba, kawai wannan kwantanci ne na marubucin.

CBN ta karyata kamun mataimakin gwamnan ta

CBN ta karyata kamun mataimakin gwamnan ta

“Baza a iya janye wa Bankin da ma’aikatunta hankali ba daga aikinta na tabbatar da tsayayyen tsarin kudade, da tattalin arzikin kasa, a wannan mawuyacin lokacin.

“Duk da haka, mutane masu aukin kaskantar da bankin da ma’aikatun ta su lura cewa akwai doka da zata kare suna da martaban bankin daga masu neman su lalata mata suna ta ko wace irin hanya.

“Saboda haka muna kira ga mambobin kafofin watsa labarai da su bi gargadi a koda yaushe da kokarin tabbatar da labarai kafin watsawa cikin hanzari," inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mambobin majalisar wakilai 2 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

A cewar wata rahoton baya,an zargi kama mataimakin gwamnan Apex Bank, Cif Adebayo Adelabu a dakin Transcorp Hilton Hotel a Abuja tare da daloli kimanin naira miliyan 200.

Jami’an EFCC sun samu labari ne kan al’amarin inda suka yi amfani da wannan daman.

Rahoton wanda gwamnati bata tabbatar ba ta ce jami’an EFCC sun shiga dakin ne, inda suka kame ma’aikacin CBN, suka sanya mishi ankwa sannan suka tafi dashi ofishin su dake Maitama a Abuja, inji NAN.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel