An sake gurfanar da yaron gidan Jonathan da wasu mutane 2 a kan billion 3

An sake gurfanar da yaron gidan Jonathan da wasu mutane 2 a kan billion 3

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta sake gurfanar da wani yaron gidan Jonathan a gaban kotu

- Ana zargin Turnah da wasu mutane 2 da kuma kamfanoni 9 da cin hanci na naira biliyan 3

- Turnah ya kasance mashawarci na musamman ga Mista Dan Abia

Hukumar ta EFCC a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, 2017 ta sake gurfanar da George Turnah, tsohon mashawarci na musamman ga Mista Dan Abia, tsohon babban daraktan hukumar ci gaban yankin Neja Delta (NDDC) da kuma wasu mutane biyu a gaban mai shari’a Ibrahim Watila na babban kotun tarayya da ke zaune a Fatakwal a jihar Ribas a kan laifuka 12 wanda ta hada da cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofis wajen wawure naira biliyan 3.4.

An gurfanar da wasu kamfanoni 9 tare da wadanda ake zargi da aika laifin.

An sake gurfanar da yaron gidan Jonathan da wasu mutane 2 a kan Billion 3

George Turnah

KU KARANTA: Naira na cigaba da kara daraja a kasuwar canji

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sauran wadanda ake zargin tare da Turban sun hada da: Ebis Orubebe da Uzogor Silas Chidiebere.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel