Shugaba Buhari ya yi sababbin nadi a babban bankin Najeriya

Shugaba Buhari ya yi sababbin nadi a babban bankin Najeriya

A yau Alhamis 5 ga watan Oktoba na shekarar 2017, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da Misis Aisha Ahmed ga majalisar Dattijai domin tabbatar da kuma tantance ta a matsayin mataimakin gwamna babban bankin kasar nan, (Central Bank of Nigeria).

Babban mai baiwa shugaban kasar shawara akan harkokin hurda da gidan jaridu da kuma al'umma Femi Adesina, ya bayyana hakan tare da cewa za ta maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan bankin wanda ya ajiye aiki tun a farkon shekarar nan.

Shugaba Buhari ya yi sabon nadi a babban bankin Najeriya

Shugaba Buhari ya yi sababbin nadi a babban bankin Najeriya

Naij.com ta ruwaito daga Adesina cewa, akwai kundin tsarin babban bankin kasa karkashin sashe na 8 shima kuma cikin sashe na daya da na biyu da ya baiwa shugaba Buhari damar aiwatar da hakan, inda kuma shugaban kasar ya ke kira ga shugaban majalisar Bukola Saraki, akan su yi tantacewar cikin gaggawa domin Misis Aisha ta samu damar fara aiki gadan-gadan.

KARANTA KUMA: Wata sabuwar cuta makamaciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda

A yayin hakan ne dai shugaban kasar ya ke neman yarjewar majalisar a rubuce, inda yake bukatar sauya kwamitin mutum hudu dake kawo tsare-tsaren kudi na babban banki. Bayan yarjewar majalisar za su shiga aiki suma a watan Janairu na shekara mai gabatowa.

Wannan mutane hudun da shugaban kasar ya bayar da sunayensu kamar haka; Farfesa Adeola Festus Adenikinju, Dakta Aliyu Rafindadi Sanusi, Dakta Robert Chikwendu Asogwa da kuma Dakta Asheikh A Madugu, za su maye gurbin tsohon kwamitin sakamakon lokacin ajiye aikinsu da ya gabato a karshen shekarar nan.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel