Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar $50,000

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar $50,000

- Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar $50,000

- Mikel Obi ya mika godiyar su ga gwamnan

- Kungiyar za ta buga kwallon kafar duniya

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom ya bawa kungiyar Super Eagles kyautar $50,000 kyauta bayan karawa da suka yi da ‘yan kwallon Kamaru.

Nigeria Football Federation (NFF) ta shaida hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar $50,000

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar $50,000

A baya dama Gwamnan ya yi wa kungiyar alkawarin dala 10,000 ga duk kwallo daya in suka ci. Bayan buga kwallon da suka yi da ‘yan wasan kwallon Kamaru ne suka ci su 4-0 a ranar 1 ga Satumba.

A ranar 1 ga Satumba kuwa suka tashi da 1-1 da suka buga kwallo da ‘yan wasan kwallon kafa na Yaounde.

Gwamnan ya kira ga ‘yan kungiyar kwallon kafar na Super Eagles a ranar Laraba da su shirya karbar kyakkyawar alherin da zai musu.

NFF ta shaida cewa idan har suka ci nasara a kwallon kafa da za a buga na duniya zasu sami wani gagarimin kyautar daga gwamnan.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

Shugaban kungiyar Mikel Obi ya mika godiyar su ga gwamnan da kuma bawa gwamnan da sauran ‘yan Najeriya karfin gwiwar cewa baza su basu kunya a wasan da za su buga a ranar Asabar ba.

'Mun san yadda kwallon nan yake da muhimmanci a gare ku don haka zamu dage don mu ga mun cika muku burinku' a cewar Mikel Obi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel