Wani mutum ya ga miyagun kwayoyi a cikin doyar da za a kai kasar waje

Wani mutum ya ga miyagun kwayoyi a cikin doyar da za a kai kasar waje

- Wani dan Najeriya ya tsinci miyagun kwayoyi a cikin doya

- An ba mutumin sakon doyar ne ya kai ma wani a kasar waje

- Kasashen waje suna daukan tsastsauran matakai akan masu shigo musu da miyagun kwayoyi kasa

Wani dan Najeriya ya tsinci miyagun kwayoyi a cikin doyar da aka bashi ya kai ma wani a kasar waje.

A wata bidiyo da aka saka shafin yanar gizo na Youtube, wani mutum daga jhar Edo ya bayyana yadda ya ga miyagun kwayoyin a cikin doyar da aka bashi ya kai ma wani a kasan waje.

Mutumin yace wanda ya bashi doyar ya rufe shi da kasa.

Wani mutum ya ga miyagun kwayoyi a cikin doyar da za a kai kasar waje

Wani mutum ya ga miyagun kwayoyi a cikin doyar da za a kai kasar waje

Da yaga kasa a jikin doyar sai yaje ya wanke ta, saboda ba zai iya tafiya da kasa a jikin doyar ba.

KU KARANTA : Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asirin asalin makiyan Buhari

Yana cikin wankewa sai ya lura ruwa na fitowa daga samar doyar, da ya duba sai ya ga rami da allurai a ciki.

Da ya janyo alluran sai yaga miyagun kwayoy a cikin doyar.

Wannan abu ne da zai iya sa a rufe mutum a kurkuku, mutane bas u da kirki. Kasashen waje suna dauka tsastsauran matakai akan masu shigo mu su da miyagun kwayoyi kasa.

Mutumin bayyana wanda ya bashi sakon doyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel