'Yan sandan jihar Ogun sun cafke miyagu 70 tare da manyan makamai

'Yan sandan jihar Ogun sun cafke miyagu 70 tare da manyan makamai

Naij.com ta kawo muku rahoton yadda hukumar 'yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wasu miyagu guda 70, wanda laifukan su sun hadar da; garkuwa da mutane, kwacen motoci, kashe-kashe na kungiyoyin asiri da kuma yin fashi da makami.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an saya wadannan 'yan ta'adda a babban ofishin 'yan sanda na Eleweran dake babban birnin Abeokuta na jihar ta Ogun karkashin gudanarwar kwamishinan 'yan sanda na jihar Ahmed Iliyasu.

Shugaban na 'yan sanda ya bayyana cewa, anyi nasarar damkar wadannan miyagu sakamakon gudanarwar jami'an na 'yan sanda mai taken kawar da 'yan ta'adda, wanda kuma a ka yi nasarar samun muggan makamai guda 29 daga gare su.

Iliyasu ya ce, akwai kimanin masu ta'addacin guda 31 a cikin su wanda suke aikata laifin asirce-asirce da tsafe-tsafe, domin kuwa an cafke su ne a yayin da suke gudanar da wannan asiri a wani Otel dake yankin Okeyidi na birnin Abeokuta.

'Yan sandan jihar Ogun sun cafke miyagu 70 tare da manyan makamai

'Yan sandan jihar Ogun sun cafke miyagu 70 tare da manyan makamai

Akwai guda 28 kuma wanda hukumar ta ke zarginsu da laifin fashi da makami, yayin da kuma aka cafke wasu biyu masu tsafi da rayukan mutane, sai kuma wasu hudu masu garkuwa da mutane.

KARANTA KUMA: Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

A cikin masu laifin fashi da makami, akwai guda daya da ya harbe wani ma'aikaci na ofishin 'yan sanda dake yankin Ogbere a ranar 13 ga watan Satumbar da ya gabata yayin da yaje kwantar da wata tarzoma a wani Otel dake yankin Itele Ijebu a jihar.

Iliyasu ya kara da cewa, akwai mutane biyu masu yiwa makabarta hidima; Jimoh Olanrewaju da Seun Babatunde da ake zarginsu da laifin siyar da sassa na jikin dan Adam ga mukabata tare da samun su da layu daban-daban wanda su ka furta cewa na asiri ne. Sai kuma wasu korarrun soji uku; Abiona Ipaye, Afolabi Olawale da Moses Ayodeji da hukumar ta cafke a garin Sango Ota bisa laifin kwacen motoci.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel