An yi ram da wani ma'aikaci da ya sace kayan aiki na naira miliyan 40

An yi ram da wani ma'aikaci da ya sace kayan aiki na naira miliyan 40

- Ana tuhumar sa da wasu mutane da yunkurin sace kayaki na naira miliyan 40 a wurin aikin sa

- Ma'aikacin ya karyata laifin da ake tuhumar sa da shi duk da makullan dakin da kayan su ke na hannun sa ne

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da wani ma'aikaci mai suna Jami'u Abioro a wata kotun Ikeja na Jihar Legas saboda yunkurin sace kayan aikin maigidansa na kudi naira miliyan 40.

Jami'u da wasu wanda ba'a samu daman kama su ba sun yi yunkurin sace kayakin wanda mallakin Kamfanin Dudu ne na naira miliyan 40.

An yi ram da wani ma'aikaci da ya sace kayan aiki na naira miliyan 40

An yi ram da wani ma'aikaci da ya sace kayan aiki na naira miliyan 40

Sifeta Ezekiel Ayorinde wanda shi ne dan sandan da ya gurfanar da Jami'u, ya ce sun aikata wannan laifi ne a ranar 15 ga watan Satumba a yankin Omole na Ojodu na Jihar Legas.

DUBA WANNAN: Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa

Mukullan dakin da kayakin suke na hannun Jami'u ne amma ya karyata laifin da ake tuhumar sa da shi. An bayar da belin sa kan naira 500,000 da malamunta biyu na wannan na wannan kudi.

Alkali mai shari'ar ta dage sauraron karan har sai ranar 16 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel