Zaben kananan hukumomi : Fayose zai rusa PDP kafin 2018 – Ambasada Dare Bejide

Zaben kananan hukumomi : Fayose zai rusa PDP kafin 2018 – Ambasada Dare Bejide

- Bejide ya zargi Fayose da son yin murdiya zabe

- Dare Bejide ya idan ba a dau mataki da wuri ba Fayose zai rusa PDP a Ekiti kafin 2018

- Tsohon jakadan ya bayyana takaicin sa game da shirun shugbanni PDP ga me da al'amuran Fayose

Tsohon jakadanan Najeriya da kasar Canada kuma jigo a jam’iyyar PDP, Amb Dare Bejide, ya fada ma shugabannin jam’iyyar PDP da su gargadi gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose akan rusa jam’iyyar kafin zaben gwaman jihar da za a yi a shekarar 2018.

Bejide ya ce Fayose ya kai zaben fid da gwani na shugabanin kananan hukumomi, da kansiloli zuwa gidan gidan gwamnan jihar dan murdiyya, yin haka zai iya durkusar da jam’iyyar idan ba a dau mataki ba.

Zaben kananan hukumomi : Fayose zai rusa PDP kafin 2018 – Ambasada Dare Bejide

Zaben kananan hukumomi : Fayose zai rusa PDP kafin 2018 – Ambasada Dare Bejide

Bejide wanda ya kasance daya daga cikin yan takarar gwamnan jihar ya ce, shirun da manyan jam’iyyar suka yi game da al’marin Fayose yana ba shi tsoro.

KU KARANTA : Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

Fayose ya mayar da shekaru dan takarar kujerar kansila zuwa 30, sai kuma shekarun dan takarar kujeran shugabanin kananan hukumomi 50.

Za a gudanar da zaben kananan hukumomi 23 ga watan Disamba na shekara 2017.

A jawabin da Bejide yayi a ranar Alhamis a Ado Ekiti, yayi kira da Shugaban kwamitin rikon kwarya dake karkashin jagorancin senata Ahmed Makarfi da ya gaggauta daukan mataki akan kurakuran Fayos kafin ya rusa jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel