Hukumar INEC ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da Osun

Hukumar INEC ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da Osun

- Hukamar INEC ta fada ranar da jam'iyyu a jihar Osun da Ekiti za su iya fara kamfen

- INEC zata gudanar da zaben gwamnonin jihar Osun da Ekiti a cikin shekarar 2018

- Shugaban hukumar INEC ya tabbatar da cewa za a kara yiwa sabbabin jam'iyyu rijista

Hukumar zabe na kasa (INEC) a ranar Alahamis ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da Osun.

Hukumar ta ce za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti a ranar 14 ga watan Yuli, na shekara 2018, sai kuma za ta gudanar na jihar Osun a ranar 22 ga watan Satumba 2018.

Hukumar INEC ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti,da Osun

Hukumar INEC ta sanar da ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti,da Osun

INEC ta ce jam’iyyu a jihar Ekiti za su iya fara kamfen din su a ranar 15 ga watan Afrailu sai kuma jam’iyyu a jihar Osun za su iya fara na su kamfen din a ranar 24 ga watan Yuni na shekara 2018.

KU KARANTA : Ranar Mallmai : Mallamai ya kamata a fara biyan albashi a Najeriya kafin majalissu – Senata Utazi

Wannan sanarwar ya fito ne daga Ofishin kwamishinan hukumar zabe na kasa, Solomon Soyebi.

Bayan haka INEC ta bayyana cewa za ta kara yi wa wasu jam’iyyu rijista.

Shugaban hukumar INEC, Ferfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya halarci wata taro da manyan jam’iyyu a ranar Laraba a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel