Naira na cigaba da kara daraja a kasuwar canji

Naira na cigaba da kara daraja a kasuwar canji

- Darajar Naira na cigaba da mikewa a kasuwa

- Bankin CBN ya dade yana dafawa Naira a kasuwa

- A jiya an wayi gari Dalar Amurka na kan N364

Yanzu mu ke samun labari daga Jaridar Punch ta kasar nan cewa Darajar Naira ya tashi daga jiya zuwa yau a halin yanzu.

Naira na cigaba da kara daraja a kasuwar canji

Manyan Jami'an babban Bankin CBN

Jaridar tace an wayi gari yau Dalar Amurka tana kan kudi N363 wanda a makon jiya yana kan N364. Kawo karshen makon jiyar dai an saida Dalar Amurka ne a kan Naira N364 bayan an bada hutun Ranar ‘Yancin kai a farkon makon yau.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da Kachikwu

A rahoton dai mun ji cewa an samu karancin kudi har Dala Biliyan $7.5 a kasafin kudin wannan shekarar. Najeriya dai na da niyyar cin bashin makudan biliyoyi a bankin Duniya da sauran bankunan kasar waje.

A jiya kun ji cewa babban bankin Najeriya na CBN ya saki Dala Miliyan 100 ga manyan ‘Yan kasuwa yayin da aka ware wasu Dala Miliyan 50 ga kananan ‘yan kasuwar kasar watau SME. A baya dai bankin ya ware Dala Miliyan 45 ga masu fita kasar waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel