Babu gudu, babu ja da baya a kan maganar sayar da filayen tashin jirgin sama; Hadi Sirika ya fadawa 'yan majalisa

Babu gudu, babu ja da baya a kan maganar sayar da filayen tashin jirgin sama; Hadi Sirika ya fadawa 'yan majalisa

- Ministan harkokin jiragen sama ya fadawa 'yan majalisa cewar babu abinda zai dakatar da batun sayar da filayen tashin jirgin saman nan guda hudu

- Sirika ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kwamitin majalisar dattijai mai kula da bangaren filayen tashin jirgin sama

- Hadi Sirika ya ce sun sanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar sufurin sararin samaniya kudirin gwamnati na sayar da filayen

Ministan harkokin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika, ya fadawa 'yan majalisa cewar babu abinda zai dakatar da batun sayar da filayen tashin jirgin saman nan guda hudu na Najeriya, domin kuwa sun cika duk ka'idojin da ya kamata a bi na sayar da su.

Babu gudu, babu ja da baya a kan maganar sayar da filayen tashin jirgin sama; Hadi Sirika ya fadawa 'yan majalisa

Hadi Sirika

Sirika ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kwamitin majalisar dattijai mai kula da bangaren filayen tashin jirgin sama. Sirika ya fadawa 'yan majalisar cewa, sayar da filayen tashin jirgin saman zai ninka kudin shiga da gwamnati take samu bayan samar da ingantaccen yanayi a filayen domin jin dadin fasinjoji.

Kwanan nan ne gwamnati ta bayyana kudirinta na sayar da filayen tashin jirgin sama na Legas, Abuja, Kano, da Fatakwal.

DUBA WANNAN: Sanata Misau masharranci ne, inji Nasiru Baba Saleh

Hadi Sirika ya ce sun sanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar sufurin sararin samaniya kudirin gwamnati na sayar da filayen tashin jirgin saman guda hudu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel