Jos: Gwamnatin Filato ta dauki sabbin malaman makaranta 5, 253

Jos: Gwamnatin Filato ta dauki sabbin malaman makaranta 5, 253

- Gwamnatin jihar Filato ta dauki sabbin malamai 5,253 a fadin jihar

- Shugaban SUBEB ya ce gwamnatin jihar ta horar da malaman makaranta fiye da 700 don samar da ilimi mai inganci

- Shugaban ya ce rashin cancantar malamai a makarantu sun kasance babbar damuwa ga gwamnati

Gwamnatin jihar Filato a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktober ta ce ta dauki sabbin malamai 5,253 a matsayin wani ɓangare na kokarin magance rashin karancin malamai a jihar.

Shugaban hukumar kula da ilimi ta farko a jihar (SUBEB) , Farfesa Mathew Sule ya bayyana hakan a Jos, babban birnin jihar cewa, gwamnatin jihar ta horar da malaman makaranta fiye da 700 don inganta halayyarsu da kuma samar da ilimi mai inganci.

NAIJ.com ta tattaro cewa, Shugaban ya ce rashin cancantar malamai a makarantun sakandare da kuma firamare sun kasance babbar damuwa ga gwamnati.

Jos: Gwamnatin Filato ta dauki sabbin malaman makaranta 5, 253

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

"Mun ziyarci makarantun firamare kuma muka gano cewa yawancin dalibai a azuzuwa na gaba ba su iya karatu ko rubutu ba”.

KU KARANTA: Masu jefa kuri'a sun dawo daga rakiyar ku, PDP ta ce ma APC

"A matsayin wani ɓangare na ƙoƙari don magance matsalar, SUBEB ta shirya wani horo na kwana 3 a watan Maris da ta gabata domin malaman makaranta 700 a fadin jihar", inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel