Kasafin kudi: Majalisar Dattawa ta gargadi fadar Shugaban kasa

Kasafin kudi: Majalisar Dattawa ta gargadi fadar Shugaban kasa

- Majalisar Dattawa tayi kira da Shugaban kasa game da kasafin kudi

- Sanatocin sun kuma nemi a kammala aikin kasafin kudin shekarar 2018

- Jiya kun ji cewa wannan shekarar ta kusa karewa ba a kai ga ko in aba

Dazu mu ke samun labari cewa Majalisar Dattawa ta nemi Gwamnatin Najeriya tayi gagaggawan kammala ayyukan kasafin kudin shekara mai zuwa.

Kasafin kudi: Majalisar Dattawa ta gargadi fadar Shugaban kasa

Majalisar Dattawa ta nemi ayi maza wajen aikin kasafi

Majalisar Dattawa ta gargadi Gwamnatin Tarayya wajen dabbaka ayyukan da ke cikin kasafin kudin bana. Sanatocin kasar ta hannun Danjuma Goje (Gombe, APC) da John Enoh (Cross River, APC) su kace ka da a sake a ware wasu wajen gudanar da ayyuka a kasar.

KU KARANTA: Idan aka sakewa Najeriya fasali za ta watse

Haka kuma Sanatocin sun kuma nemi a kammala aikin kasafin kudin shekarar 2018 da wuri saboda gudun bata lokaci kamar yadda aka saba samu a baya. Majalisar ta kuma yi kira a toshe duk wata rarar baraka a Ma’aikatun kasar.

Kusan duk shekara akan samu takaddama tsakanin 'Yan Majalisar da Shugaban kasa wanda hakan ta sa Sanatocin kasar su ka kira Shugaban kasa ya dauki mataki wannan karo don badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel