Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose

Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose

- Makarfi ya bayyana cewar neman takarar shugabancin kasar Fayose ya sabawa shawarar jam'iyyar PDP

- Makarfi yayi watsi da jita-jitar cewar wai PDP zata bawa Atiku takara matukar ya amince ya dawo jam'iyyar

- Jam'iyyar ta bayyana cewar dan takarar ta daga arewa zai fito

Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Makarfi, ya bayyana cewar neman takarar shugabancin kasar gwamnanan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya sabawa shawarar jam'iyyar PDP. Makarfi ya bayyana haka ne jiya a Kaduna yayin wata ganawa da manema labarai.

Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose

Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose

Makarfi ya ce "Shi, Fayose, yayi gaban kansa ne kawai, amma bada sahalewar jam'iyya ya kaddamar da takarar sa ba. Matsayin jam'iyyar PDP na fitar da dan takarar shugabancin kasa daga arewa bai canja ba".

Hakazalika Makarfi yayi watsi da jita-jitar cewar wai PDP zata bawa Atiku takara matukar ya amince ya dawo jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Hukumar RSS ta tsinci wasu yara guda 2 a jihar Legas

Ayodele Fayose dai ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyarsa ta PDP a zaben shekarar 2019 duk da cewar jam'iyyar ta bayyana cewar dan takarar ta daga arewa zai fito.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel