Rundunar yan sanda ta kama jami’ai 2 dake saida bindigogi ga yan fashi da masu satar mutane

Rundunar yan sanda ta kama jami’ai 2 dake saida bindigogi ga yan fashi da masu satar mutane

Rundunar yan sandan Najeriya wanda hedkwatansu ke Umuahia, sun kama wasu koporal guda biyu bisa laifin sayar da bindigogi ga yan fashi da masu satar mutane da masu kisan kai.

A cewar Sahara Reporters wadanda aka kama sune Mbara Udochukwu (Force No. 46255) da kuma Glory Eke (Force No. 44269).

Udochukwu na aiki tare da rundunar sashi na 9, Umuahia, yayinda Eke ke aiki da sashin Isiala Mbaino dake jihar Abia.

Har ila yau an sanar da kamun Jude Madu, wani tsohon koporal mai lamba 462551.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi a arewa (hotuna)

An kama Madu a ranar 9 ga watan Satumba sannan kuma an same shi da waya mallakar Reverend Father Cyricus Onunkwo na cocin Orlu Catholic Diocese, wanda aka sace a ranar 1 ga watan Satumba sannan aka samu gawarshi a washegari.

Sannan kuma, Madu ya amince da jagorantar mutane shidda da suka sace malamin cocin tare da kashe shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel