Ba mu goyi bayan ayi wa Najeriya garambawul ba – APGA

Ba mu goyi bayan ayi wa Najeriya garambawul ba – APGA

- Jam’iyyar A.P.G.A ba ta goyon bayan a yi wa Najeriya garambawul

- A cewar ta Gwamnoni za su ci karen su babu babbaka idan aka yi haka

- Jam’iyyar tace wasu Gwamnonin Jihohi kasar ba su da aiki sai barna

Za ku ji cewa Jam’iyyar adawa ta APGA tace idan aka yi garambawul zai ba Gwamnonin Jihohi matsayi fiye da kima a Najeriya.

Ba mu goyi bayan ayi wa Najeriya garambawul ba – APGA

Garambawul zai ba Gwamnonin Jihohi matsayi fiye da kima - APGA

Jam’iyyar APGA tace wasu Gwamnonin Jihohin kasar ba su da aiki sai barna da dukiyar da Gwamnatin Tarayya ta aika masu ba tare da wani bin ka’ida ba. APGA tace Gwamnonin za su maida Majalisar Jihohi da kananan Hukumonin kasar har da Kotu a hannun su.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya raba kan 'Yan kasa - Okorie

APGA ta bayyana cewa idan Shugaba Buhari ya sake ya yarda da batun to Najeriya za ta dagargaje. A cewar ta da abin kwarai ne da Jam’iyar PDP ta sakewa kasar fasali a lokacin da tayi mulki. Jam’iyyar dai tace hakan kurum zai karawa Gwamnoni karfi ne babu gaira babu dalili.

Jam’iyyar adawa UPP Chekwas Okorie ya soki mulkin Shugaba Buhari ayi wa kasar garambawul idan har ana so a cigaba wanda a cewar sa Shugaba Buhari ya bar gini tun ranar zane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel