Tun dama Buhari ba shi da sha'awar ganin Kachikwu - Aisha Yesufu

Tun dama Buhari ba shi da sha'awar ganin Kachikwu - Aisha Yesufu

- Aisha Yesufu ta soki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan abin da aka yiwa ministan harkokin man fetur, Ibe Kachikwu

- Aisha ta ce tun dama shugaba Buhari ba shi da sha'awar ganin Kachikwu

- Aisha ta bayyana cewa shugaba Buhari ya kamata a ce yana neman Kachikwu

Shugaban kungiyar “BringBackOurGirls”, BBOG, Aisha Yesufu ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan abin da aka yiwa ministan harkokin man fetur, Ibe Kachikwu.

Ta jaddada cewa tun dama shugaba Buhari ba shi da sha'awar ganin Kachikwu.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Aisha ta yi wannan ikirarin ne yayin da take mayar da martani game da wasikar Kachikwu zuwa ga shugaban kasa, inda ya zarge babban darakta na kamfanin albarkatun man na Najeriya, NNPC, Maikanti Baru a kan aikata ba daidai ba.

Tun dama Buhari ba shi da sha'awar ganin Kachikwu - Aisha Yesufu

Shugaban kungiyar “BringBackOurGirls”, BBOG, Aisha Yesufu

Kachikwu ya zargi GMD na NNPC na bayar da kwangilar da ya zarce dala biliyan 26 ba tare da amincewar kwamitin ba.

KU KARANTA: Rikicin Baru da Kachikwu: Shugaba Buhari zai dauki matakin binciken NNPC

Ministan ya ci gaba da cewa an hana shi damar ganin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Da take magana akan batun a shafinsa ta Twitter, Aisha ta rubuta cewa: "Ku daina cewa Kachikwu ba shi da damar ganin shugaban kasa. Kawai shugaban ba ya son ganin Kachikwu ne”.

“Kachikwu ne karamar minista na ma'aikatar, wanda ke ba Najeriya mafi yawan kudin shiga, kuma Buhari ne babban ministan”.

"Shugaba Buhari ya kamata a ce yana neman Kachikwu, tun da karamar ministan na karkashin sa ne”, inji ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel