Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Rundunar Soji ta 151 da Bataliya a 202 dake karkashin aikin ‘Operation Lafiya Dole’ sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya a ranar Laraba4 ga watan Oktoba da misalin karfe 10 na safe.

Sojojin sun yi ma yan ta’addan kwantan bauna ne a daidai kauyen Firgi-Pulka dake karamar hukumar Bama na jihar Borno, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Rashin lafiyar Warangis: Furodusa a Kannywood ya mayar da martani

Yayin harin an yi musayar wuta tsakanin Sojojin da yan ta’addan, inda aka fi karfin yan ta’addan, nan da nan ba tare da bata lokaciba suka zura a guje, suka yi watsi makamansu.

Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Babur

Cikin kayan da Sojojin suka kwato akwai babur guda daya, sai makamin baro jirgin sama, tare da bindigu guda 3 kirar AK 47, alburusai da kuma bama bamai guda 5 da basu fashe ba.

A wani labarin kuma, a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba, da misalin karfe 6 na yamma, wasu yan kunar bakin wake su uku sun nufi wani sansanin yan gudun hijira, amma Sojojin Najeriya sun dakatar dasu, inda suka tada kansu.

Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Makamai

Wannan jarumta da Sojojin suka nuna ya kiyaye faruwar barna mai muni wanda Allah kadai yasan iya abin da za’a yi asara na rayuka da dukiyoyi.

Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Makamai

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yan Boko Haram sun saci mijin wannan matar, kalla NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel