NNPC: Kamata yayi Kachikwu ya ba Baru ayar tambaya - Tsav

NNPC: Kamata yayi Kachikwu ya ba Baru ayar tambaya - Tsav

- Rashin jituwa dake gudana tsakanin Dr. Ibe Kachikwu da manajan daraktan kamfanin NNPC ya kai ga shawarwari da dama

- Tsohon kwamishinan yan sanda na jihar Legas, Abubakar Tsav, ya ce ya kamata Kachikwu ya tuhumi Baru

- Tsav ya lura cewa matakin Baru yana iya kasancewa saboda kusancin shi ga Shugaba Muhammadu Buhari

Mutane da dama sun shiga rashin jituwa dake tsakanin manajan daraktan kamfanin NNPC, Maikanti Baru, da karamin ministan fetur, Dr. Ibe Kachikwu.

Tsohon kwamishinan yan sanda na jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsav, ya bayyana cewa kamata yayi Dr. Kachikwu ya tuhumi Baru kafin yanzu.

Har ila yau yace kamata yayi ministan ya rubuta wa Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), da tambayan shi kan me yasa irin abubuwan nan suka faru.

NNPC: Kamata yayi Kachikwu ya ba Baru ayar tambaya - Tsav

NNPC: Kamata yayi Kachikwu ya ba Baru ayar tambaya - Tsav

A cewar jaridar Vanguard, Tsav ya lura cewa matakin Baru yana iya kasancewa saboda kusancin shi da shugaba Buhari, wanda ba dai-dai bane.

KU KARANTA KUMA: NNPC: Kachikwu should give Baru a query - Tsav

“Ina tunanin GMD na kamfanin NNPC ya bayyana babbar kuskure saboda ya kasance mai amshi zuwa ga minista.

“Da nine a matsayin ministan, da na tuhumi GMD da bukatar ya bayyana me yasa abubawa suka faru haka.

“Kuma tuhumar har ila yau zai je ga Sakataren Gwamnatin Tarayya. Idan mutumin yayi hakan ne saboda kusancin shi ga shugaba, ba dai dai bane tunda shugaban ya amince da Kachikwu kuma dalilin da yasa ya sanya shi a matsayin minista kenan.

“Da nine a matsayin shugaba, ko in yi transfa dinsa ko in bashi izinin aika sakonni cewa ba dai dai bane rage darajar takun wadanda suke sama da kai.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel