'Yan Najeriya sun hada kai don samun galaba a kan Boko Haram

'Yan Najeriya sun hada kai don samun galaba a kan Boko Haram

- Najeriya ta horar da sojojin ta a kan kare hakkin bil'Adama wajen yaki da ta'addanci

- Ta yi kira ga malaman addini don su wayar da kan al'umma ta yadda Boko Haram ke diban ma'aikata

- 'Yan Najeriya sun bada hadin kai jwarai da gaske shi ya sa aka samu lafiya a yankin Arewa-maso-gabas

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan Najeriya sun hade kai don su ga sun ci galaba a kan ta'addancin Boko Haram. Ambasada Hussein Abdullahi ne ya fadi haka lokacin da ya wakilci Najeriya a taron 'Yadda za'a magance ta'addanci a duniya' da aka yi a New York, Amurka.

'Yan Najeriya sun hada kai don samun galaba a kan Boko Haram

'Yan Najeriya sun hada kai don samun galaba a kan Boko Haram

Ya ce gwamnatin Najeriya ta kaddamar da ma'aikata guda ta magance ta'addanci (NACEST), kuma an yi kira ga kowacce ma'aikata da su basu hadin kai.

NACEST na kira ga malaman addinai da su yi kira ga daliban su da al'umma gaba daya da su wayi yadda Boko Haram ke wanke kwakwalwar mutane don su shiga ta'addanci.

Saboda hadin kan da aka bawa wannan ma'aikata da gwamntin kasa ya kawo raguwar ta'addancin Boko Haram kwarai da gaske.

"Sojojin Najeriya sun ci nasara, kuma sun kwace duk wata karamar hukumar da Boko Haram suka kafa tutar su. Mazaunan yankunan kuma a yanzu suna nan suna walwalar su ta yau da kullum ba tsangwama."

"Gwamnatin Najeriya ta horar da sojojin ta a kan yadda zasu yaki ta'addanci a ta cikin zagayen birni, fada ba makami, da kuma kula hakkin dan Adam."

DUBA WANNAN: Kungiyar kwadago ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganar karin albashi

"Kari kuma, an rage lokacin da ake dauka kafin a shari'anci wadanda aka kama a zargin 'yan Boko Haram ne. Wadanda suka tuba kuma, an tsayar da hanyoyin da za'a sake musu wankin kwakwalwa don shigar da su cikin al'umma na gari."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel