Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

- Buba Galadima wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya ce jam'iyyar ta cancanci a rushe ta

- Ya ce jam'iyyar ta gaza cika koda daya daga cikin alkawuran da ta daukan ma 'yan Najeriya

- Duk da kasancewar jam'iyyar na da matsaloli, ya bayyana burin sa na daidaituwar ta

A jiya ne sashin hausa na BBC ta yi hira da Buba Galadima wanda jigo ne a jam'iyyar APC. A hirar ta su ne ya ce in da shi ne Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC, da ya rushe jam'iyyar ta APC.

Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

Jam'iyyar APC ta cancanci a rushe ta, inji Buba Galadima

Ya fadi hakan ne yana me kafa hujja da kunnen uwar shegu da masu tafiyar da jam'iyyar suke ma dokoki na jam'iyyar. Ya kara da cewa tun kafa jam'iyyar shekaru 3 da suka wuce ba'a taba yin zama na amintattun mutane masu tafiyar da jam'iyyar ba.

Ya ce ba a taba tuntubar daya daga cikin dattawan da suka kafa jam'iyyar ba da sunan neman shawara ko makamancin sa. Bugu da kari, jam'iyyar ta kasa cika koda guda daya daga cikin alkawuran da ta daukan ma 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

Sai dai kuma Galadima ya bayyana burin sa na daidaituwar jam'iyyar ko da kuwa ba da tarayya da Muhammadu Buhari ba.

''Na ki jinin yadda mutane ke daura wanzuwar APC a wuyan mutan daya; jam'iyyar ta mu ce gaba dayan mu, mu 'yan Najeriya. Siyasa da karfin iko ba masu daurewa bane, don haka dole mu lura da abun da zai kai ya komo.'' In ji Galadima.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel