Biyafara: Gwamnonin kudu maso gabas matsorata ne – Inji lauyan Kanu

Biyafara: Gwamnonin kudu maso gabas matsorata ne – Inji lauyan Kanu

- Lauyan shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara, IPOB ya soki lamirin gwamnonin yankin kudu maso gabas

- Ejiofor ya ce Gwamnonin kudu maso gabas matsorata ne

- Lauyan Kanu ya ce sojoji na aiwatar da manufar gwamnatin tarayya da na shugabanin arewa

Mista Ifeanyi Ejiofor, lauyan shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu, ya bayyana wasu gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya a matsayin matsorata.

Ejiofor ya gabatar da jawabin ne yayin da ya lura cewa gwamnonin ba su goyi bayan gwagwarmaya ta IPOB ba domin tabbatar da matsayin siyasar su.

Lauyan shugaban na IPOB, ya yi gargadin cewa za a yi waje da shugabanin siyasa na yanzu a yankin kudu maso gabas a lokacin zaben 2019.

Biyafara: Gwamnonin kudu maso gabas matsorata ne – Inji lauyan Kanu

Shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu

Da yake jawabi ga majiyar NAIJ.com, Ejiofor ya ce, "Gwamnonin kudu maso gabas ba su da iko su ce IPOB wata kungiya ce ta ta'addanci kuma wannan gaskiya ne. Na la’ane wannan matsayin su, amma sun janye, suna cewa ba su taba fada haka ba. Bayanan su na siyasa ne kawai don samun goyon baya daga gwamnatin tarayya”.

KU KARANTA: Sauran Lauyoyi sun yi kira a damke Lauyan Nnamdi Kanu

“Za mu shirya matasan yankin don su fito a shekarar 2019 don kawar da dukkan 'yan siyasar".

Da yake jawabi kan zargin mamaye gidan Kanu da sojoji suka a ranar 14 ga watan Satumba, Ejiofor ya nace cewa sojojin na aiwatar da manufar gwamnatin tarayya da na shugabanin arewa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel