Rashin lafiyar Warangis: Furodusa a Kannywood ya mayar da martani

Rashin lafiyar Warangis: Furodusa a Kannywood ya mayar da martani

Sanannen Furodusan nan na Fina finan Kannywood, Usman Mu’azu ya musanta zargin da yaron shahararren jarumin nan, Malam Warangis, Ibrahim Warangis yayi, na cewa wai yan Fim basu taimakesu ba.

Usman yace wannan magana ba haka take ba, saboda da wasu daga cikin yan Fim suna ba Warangis tallafi iya kokarinsu, inda ya kara da cewa, wasu sun bashi taimakon a fili, wasu kuma sun boye taimakon da suka yi masa.

KU KARANTA: Rashin imani: Yadda wani dan fashi yayi ma sa’an Kakansa fashi, kuma ya kashe shi

Jaridar Rariya ta ruwaito Usmana yana kokawa kan yadda aka yi ma yan Fim kudin goro ana cewa wai duk basu taimaka ma Malam Warangis ba, wanda ke fama da cutar koda tun da dadewa.

Rashin lafiyar Warangis: Furodusa a Kannywood ya mayar da martani

Warangis

“Ni da kai na, wata jaruma data bukaci in boye sunanta ta sanya na aika masa da kudi da kuma kayan abinci, haka zalika Ali Nuhu, Sadik Sani, Zainab Ziya’u, Sa’eed Nagudu duk sun taimaka masa.” Inji Usman.

Usman ya bada tabbacin akwai wasu yan Fim da suka shiga mawuyacin hali fiye da na Warangis, kuma yan Fim suna taimaka musu, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yaya Najeriya take a yau? kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel