Ranar Mallmai : Mallamai ya kamata a fara biyan albashi a Najeriya kafin majalissu – Senata Utazi

Ranar Mallmai : Mallamai ya kamata a fara biyan albashi a Najeriya kafin majalissu – Senata Utazi

- Senata Utazi ya nuna takaici akan yadda aka dauki al'amarin mallamai a Najeriya da rashin muhimmanci

- Dan majalissar yayi kira da gwamnati Najeriya da ta gaggauta inganta rayuwa mallamai a kasar

- Shugaban Majalissar Dattawa Bukola Saraki yayi alkwarin zama na musamman dan tattauna yadda za a inganta rayuwar mallamai a Najeriya

A yau ne 5 ga watan Oktoba ake bikin ranar Mallamai a duniya, Senata mai wakiltar mazabar Arewacin Enugu, Chukuwuma Utazi ya ce mallamai yakamata a fara biya albashi a Najeriya kafin yan majallisu da sauran ma’aikata.

Dan majalissar ya nuna takaici akan yadda aka dauki al’amarin mallamai da rashin mahimmaci a Najeriya, babu wanda yake son aikin mallanta a Najeriya.

Ya kalubalanci manyan yan Najeriya dake bin mallaman kasashen waje da kudade masu yawa wajen neman ma yayan su ilimi, amma sun bar mallaman Najeriya a cikin halin kakanikayi.

Ranar Mallmai : Mallamai ya kamata fara biyan albashi a Najeriya kafin majalissa – Senata Utazi

Ranar Mallmai : Mallamai ya kamata fara biyan albashi a Najeriya kafin majalissa – Senata Utazi

Ina kira da gwamnatin Najeriya da ta inganta rayuwa mallamai saboda al’umma ta dauki aikin mallanta da muhimmaci.

KU KARANTA : Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

Dan majjalisar ya nuna damuwar shi akan yadda rashin biyan albashin mallaman makaranta akan lokaci, wanda wannan ya sa mutane ba son aikin.

Senata Utazi ya ce idan ba a gagguta dauka mataki akan wannan al’amari ba, za a wayi gari babu mallami ko daya a Najeriya.

Shugaban majalissar dattawa, Dakta Bukola Saraki ya tabbatar da cewa, za ayi zama na musaman dan tattauna yadda za a inganta aikin mallanta Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel