Kachikwu zai gana da Buhari kan rikicin NNPC

Kachikwu zai gana da Buhari kan rikicin NNPC

Kwanaki biyu bayan billowar wasikar sa ga manema labarai, karamin minstan man fetur, Ibe Kachikwu zai gana da shugaba Muhammadu Buharia a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba ba wai a yau ba kamar yadda aka rahoto a baya.

A cewar jaridar Premium Times wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za'a fara ganawar ne da misalin karfe 11:3o na safiyar Juma'a.

Kachikwu ya aika da wata wasika ga shugaban kasar, inda yayi korafi akan rashin da’a da kuma zargin rashawa ga manajan darakta na kamfanin NNPC, Maikanti Baru.

Ministan ya kuma bukaci shugaba Buhari da yayi gaggawan daukar mataki don ceto kamfanin NNPC akan wani kwangilan jabu na naira triliyan 9 da sa hannun Baru.

KU KARANTA KUMA: Yar Sarkin Kano Gimbiya Siddika ta haifi danta na fari tare da mijinta (hotuna)

Mista Kachikwu yace yana ganin akwai bukatar jan hankalin shugaban kasar ga rashin bin doka saboda suna iya wasa da al’amarin cigaban sashin man fetur na kasar.

Ya kuma ce ya yanke shawarar rubuta wasika ne saboda bai samu damar ganawa da shugaban kasar ido da ido ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel