Shugaba Buhari yayi shiru yayinda badakalar naira triliyan 9 ya billo a kamfanin NNPC

Shugaba Buhari yayi shiru yayinda badakalar naira triliyan 9 ya billo a kamfanin NNPC

- Shugaba Buhari yayi shiru duk da abun kunyan da ya billo a kamfanin NNPC

- Shugaban kasar ne jagoran yaki da rashawa kuma shi ke rike da matsayin ministan man fetur

- Ibe Kachikwu, karamin minstan man fetur, a wata wasika day a aika ga shugaba Buhari ya bayyana ayyukan Maikanti Baru, manajan darakta na kamfanin NNPC wadanda ked a alamun tambaya

Shugaba Muhammadu Buhari bai yi jawabi ba kan zargi mai tsanani da aka yi kan kin yin amfani da tsarin kwangila na kimanin N9 tiriliyan a kamfanin NNPC, wanda ya bayyana fiye da sa’o’i 24 a wata takarda dake dauke da zargin.

Masu magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina da Garba Shehu, basu daga kira da aka yi wa lambobinsu ba ko amsa sakonni ta wayar salula kan al’amarin duk da damuwa da yan Najeriya masu himmar aiki suka nuna.

Karamin Ministan man Fetur, Ibe Kachikwu, ya bayyana daki-daki kan cinikin mai alamar tambaya a lokacin da ya tuntubi shugaban kan ayyukan Manajan Daraktan kamfanin NNPC Maikanti Baru.

Shugaba Buhari yayi shiru yayinda badakalar naira triliyan 9 ya billo a kamfanin NNPC

Shugaba Buhari yayi shiru yayinda badakalar naira triliyan 9 ya billo a kamfanin NNPC

A ranar 30 ga watan Agusta ne, Mista Kachikwu rubuta wata wasika inda ya ce Baru ya kubuta daga tsari ba da kwangila a jere har na kudi biliyan $25 ko tiriliyan N9 a rinjayar canjin farashi daga N360 zuwa dala daya, da gargadi kan sakamako da matakin zata kawo idan aka bari ta tsaya.

Wasikan ta bayyana ne a yanar gizo a ranar Talata, amman babu wanda yayi ikirarin bayyana al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Mahajjata 16 da suka yi tattaki daga Kebbi zuwa jihar Niger don ganin rubutu larabci sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Mista Kachikwu ya bada lissafin kwangila da aka bayar ba tare da neman shawarar ma’aikatar man fetur ko hukumar kamfanin NNPC ba; har da biliyan $10 na kwangilar danyen mai; biliyan $5 na kwangilan kasuwanci siya da siyarwa (DSDP) da biliyan $3 na kwangilan bututun man AKK.

Har ila yau ya ce an bada kwangilan biliyan $3 ga bangarori daban daban na kudade da ake warewa da wassu biliyan $3-4 na kwangilan samar da sabis naNPDC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel