Samari uku zasu sha bulala saboda zaman kashe-wando

Samari uku zasu sha bulala saboda zaman kashe-wando

- An hana zaman kashe-wando a wajen

- An taba kama su, aka gargade su sannan aka sake su

- Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce in aka sake kama su da ko wanne irin laifi za su dandana kudar da ta fi haka

A ranar Laraba wata kotu a Karmo, Abuja, ta yankewa wasu samari uku hukuncin bulala shida-shida saboda zaman kashe wando da aka kama su suna yi a lambun Hill Top, da ke kallon kasuwar Wuse a Abuja.

Samari uku zasu sha bulala saboda zaman kashe-wando

Samari uku zasu sha bulala saboda zaman kashe-wando

Samarin sune Daniel Lucky, Aliyu Ahmed, da Badaru Lawal.

Wacce ta shigar da karar, Florence Avhioboh, ta ce dama 'yan sanda sun taba kama su da wannan laifi amma suka yi musu kashedi a kan kar su sake. Amma a ranar 30 ga watan Satumba, sai 'yan sandan suka sake kama su a wajen.

Da aka tambaye su mai suke yi a wajen, sai suka fara kame-kame. Kan kace me 'yan sanda kuwa suka yi awon gaba da su.

DUBA WANNAN: Babbar matsalar masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood

Samarin sun amsa laifin su a gaban alkali Abubakar Sadiq, sannan kuma sun roki ayi musu rangwame a kan hukuncin da za'a dauka, da alkawarin ba zasu kara ba. Alkalin ya gargade su da kada a sake kawo masa su gaban shi saboda wani laifi. Daga bisani ya ce ayi musu bulala shida-shida don kore gaba.

Dokar da suka karya tana cikin Sashe na 199 na kundin laifuffuka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel