Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

- Shugaban cibiyar kula da aikin malunta ta kasa ya yi raddi ga malaman da basu san makamin aikinsu ba

- Ajiboye yace jihar Kano ce kan gaba wajen tarin malami da basu da kwarewa

- Ya ce akalla akwai malamai sama da 25,000 da basu kware a kan aikin su ba a jihar Kano kawai

- A yanzu haka cibiyar ta TRCN na kokarin tura malamai manyan makarantun koyan aikin malunta da kwalejojin kimiyya da fasaha domin gogewa a harkar karantarwan

Shugaban cibiyar kula da aikin malunta ta kasa Josiah Ajiboye ya bayyana cewa jihar Kano kadai na da yawan malamai sama da guda 25,000 da basu kware a kan aikinsu na malanta ba

Ajiboye ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja gurin wani taro da aka gudanar domin tattaunawa kan yadda za a inganta aikin malunta a fadin kasar.

A cewar sa: “Sama da malamai 300,000 cikin 700,000 dake karantarwa a makarantun kasar nan basu da kwarewa akan aikin malunta.”

Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

Jihar Kano ce kan gaba a yawan malaman da basu kware a aikin malunta ba -TRCN

Yace jihar Kano na kan gaba wajen yawan malamai da basu kware a aikin malunta ba.

KU KARANTA KUMA: Nan da kwanaki 90 ku yi mana maganin fasa kauri – Hamid Ali ya bada oda

Ya kara da cewa cibiyar TRCN na kokarin tura malamai manyan makarantun koyan aikin malunta da kwalejojin kimiyya da fasaha domin gogewa a harkar karantarwan.

Bayan haka ya koka ga yadda wasu jihohi a kasarnan basu damu da jindadin malamai ba in da wasu harta albashi ma ke musu wuyan biyan malamai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel