Dalilin da zai sa mu tursasa Buhari sake neman kujerar shugabannci karo na biyu - Kungiya

Dalilin da zai sa mu tursasa Buhari sake neman kujerar shugabannci karo na biyu - Kungiya

- Kungiyar yakin neman zabe na Buhari (BCO) ta bayyana abinda yasa shugaba Buhari zai sake takara a zaben 2019

- Kungiyar BCO ta ce Buhari zai nemi a sake zaben shi saboda gagarumin nasarori da ya samu wajen kai Najeriya matsayi mai girma

- Kungiyar ta ce manoma fiye da miliyan 2.8 sun amfana daga daya daga cikin manufofi da shugaban ya kafa

Kungiyar yakin neman zabe ga Buhari ta sanar cewa mambobin ta suna aiki don ganin sun “tilasta shugaba Muhammadu Buhari ga neman a sake zabin shi a 2019.”

Shugabannin kungiyar BCO sun ce suna bukatan Buhari ya sake neman a zabe shi saboda, gagarumar nasarori wajen daukaka Najeriya ta hanyar ajandar shi, maunufofin shi da yaki da rashawa da ta’addanci.

Dalilin da zai sa mu tursasa Buhari sake neman kujerar shugabannci karo na biyu - Kungiya

Dalilin da zai sa mu tursasa Buhari sake neman kujerar shugabannci karo na biyu - Kungiya

Rahotanni sun zo cewa Danladi Pasali, shugaban kungiyar ta kasa , a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba ya bayyana haka a jihar Filato.

KU KARANTA KUMA: Danjuma, Abdulsalami sun aika sako ga yan Najeriya dake neman ballewa

Pasali yace manufofin Buhari irin manufar bada tallafi dake karkashin babban bankin kasa (CBN) da ta ware kudi biliya N220 don aro ga manoma ta samu gagarumar nasara.

Shugaban kungiyan y ace manoma fiye da miliyan 2.8 ne suka amfana daga wannan shirin da wassunsu da suka yi gine ginen gidaje ga iyalensu da biya wa kahunansu kudin hajji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel