Danjuma, Abdulsalami sun aika sako ga yan Najeriya dake neman ballewa

Danjuma, Abdulsalami sun aika sako ga yan Najeriya dake neman ballewa

- Janar Abdulsalami Abubakar yayi kira ga yan Najeriya da su hada kai

- Tsohon shugaban kasar yace wannan ita ce hanya guda da cigaba zai iya zuwa

- Danjuma ma ya nuna goyon baya ga yin garambawul

Tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya aika sako ga matasan Najeriya inda yayi kira gare su da su hada kawunansu domin Najeriya ta samu cigaba.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa Abdulsalami yayi magana a wajen kaddamar da makarantar Emeka Anyaoku’s Institute of International Studies and Diplomacy a jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, jihar Anambra a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba.

Tsohon shugaban kasar yayi kira ga matasa da su yi gini a kan manufofin da magabata suka gina domin ganin cewa kasar bai rabu ba.

Janar Theophilus Danjuma wanda shima ya halarci taron ya nuna goyon bayansa ga kira ga yin garambawul. Ya kuma bayyana cewa ya zama dole a cimma wannan ba tare da rikici ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari na kewaye da mutane dake jan kambun mulki domin ra’ayin kansu – Shehu Sani

Janar Ike Nwachukwu ma ya yarda da cewa ya zama lallai a cimma kira ga garambawul ba tare da rikici ba.

Ya yi kira ga matasa da karda su bari kasar ta tabarbare tare da tunasar dasu cewa Najeriya tayi yaki mai daci a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel