Rashin imani: Yadda wani dan fashi yayi ma sa’an Kakansa fashi, kuma ya kashe shi

Rashin imani: Yadda wani dan fashi yayi ma sa’an Kakansa fashi, kuma ya kashe shi

Wani Dan fashi mai suna Moses Angah ya tabbatar ma yansandan jihar Kaduna yayin da suke gudanar da bincike kan shi ya hallaka wani sa’an Kakansa bayan yayi masa satar kudi N80,000.

Kwamishinan Yansandan jihar Agyole Abeh ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da miyagun mutane da suka aikata laifuka daban daban a jihar Kaduna ga manema labaru a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Tataɓurza a majalisa: Majalisar dokokin jihar Kano ta ɓara dangane da sallamar Abdulmuminu

Jaridar Daily Post ta ruwaito kwamishinan yana fadin sun kama da dama daga cikin miyagun mutanen ne yayin da suke cikin aikata laifukan da ake tuhumarsu akai, sauran kuma sunkama su ne ta hanyar wayoyin da suka sace.

Rashin imani: Yadda wani dan fashi yayi ma sa’an Kakansa fashi, kuma ya kashe shi

Yansanda

A yayin bajekolin masu laifukan, an yi hira da wani dna fashi daya kashe wani dattijo mai shekaru 80, wanda yayi kaka da shi bayan ya kwace masa naira dubu 80.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito dan fashin yana fadin cewa talauci ne ya kai shi ga aikata hakan, inda yace a daren ya shiga gidaje guda biyu ba tare da ya samu sa’an yi musu fashi ba, daga nan ne ya fada gida na uku, inda ya tarar da dattijon tare da matarsa suna kwance.

“Don na bashi tsoro, sai na buga masa rodi a kai, inda na cigaba da dukan matarsa, har sa da ta dauko min dubu 80, da kuma wayar hannu, sai na daina dukanta.” Inji barawon.

“Washe gari sai na siyar da wayar N10,000, ta wayar ne yansanda suka kama ni, bayan sun kamo wanda na siyar mawa, shi kumwa ya kirani da nufin zai biyani kudin wayar, a haka ne suka kama ni. Gaskiya nayi nadamar abin dana aikata.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Kun san menene manufar Biyafara? kalli NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel