Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna takaici da alhini kan rashin amininsa AVM Mukhtar Muhammad, wanda ya rasu a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.

Kaakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu yace shugaba Buhari ya bayyana haka ne ciin wata wasika daya aika wakilan daya tura jihar Kano da Jigawa don yi masa ta’aziyya.

KU KARANTA: Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito wasikar shugaban kasar an mika ta ga gwamnan jihar Abubakar Badaru, wanda shi kuma ya mika ma Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sunusi.

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Tawagar Buhari

Tawagar shugaban kasa ta kunshi ministan tsaro Mansur Dan Ali, ministan Ilimi Adamu Adamu, ministan ruwa, Suleiman Adamu, ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, Garba Shehu, Musa Haro duk a karkashin jagorancin Abba Kyari.

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Tawagar tare da Sarkin Dutse

Wasikar tana cewa “marigayi Mukhtar aminina ne, kuma soja ne mai kokari, duk mutanen da suka yi mu’amala da shi sun tabbatar da gaskiyarsa, haka ma a siyasa, mutum ne mai nuna jajircewa.”

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Jana'izar

Sauran yan tawagar shugaban kasa sun hada da ministan sufurin jirgi, Hadi Sirika, Ya’u Darazo, Sha’aban Sharada da kuma shugaban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar.

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Yayin mika wasikar ga Sarki

Tawagar ta tsaya a jihar Kano, inda ta hadu da gwamnan jihar Kano da Sarki Muhammadu Sunusi, sa’annan suka halarci jana’izar marigayin.

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Zaman makoki

Rasuwar AVM Mukhtar: Shugaba Buhari yayi jimami tare da nuna alhini

Abba Kyari, Badaru da Ganduje

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Farashin mai ya karye, kalli NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel