Yadda Moro suka rabe naira miliyan 675 na kudin masu neman aiki

Yadda Moro suka rabe naira miliyan 675 na kudin masu neman aiki

A ranar Larabar da ta gabata, wasu mutane biyu sun bayyana a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja domin bayar da shaidar yadda Abba Moro da makarrabansa suka yi bushasharsu da Naira Miliyan 675 na mutane 675, 675 na masu neman aikin hukumar kaura ta kasa (Nigerian Immigration Service, NIS).

Wannan mutane biyun sun tsaya a gaban kotu a mastsayinsu na masu bayar da shaida na biyar da na shida akan shari'ar dake wakana ta tsohon ministan cikin gida Abba Moro, sakamakon tuhuma da kuma zarginsu da ake yi da aikata laifukan cin hanci da rashawa tare da zambar kudi.

Hukumar EFCC ta na tuhumar wannan mutane ukun wadanda suka hadar da Moro, tsohuwar sakatare ta dindindin ta ma'aikar cikin gida Misis Anastasia Daniel-Nwobia da kuma mataimakin Darakta na ma'aikatar Mista Femi Alayebami.

Yadda Moro suka rabe naira miliyan 675 na kudin masu neman aiki

Yadda Moro suka rabe naira miliyan 675 na kudin masu neman aiki

Akwai kuma kamfanin Drexel Tech. Nigeria Limited da hukumar take tuhuma, sakamakon ruwa da tsaki da kamfanin yayi wajen aiwatar da gudanarwar harkar daukan masu neman aikin na hukumar ta Kaura.

KARANTA KUMA: Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

Hukumar EFCC ta na zargin su ne bisa aikata laifin zamba na kudi na masu neman aikin har guda 675,675 inda kowanen su ya biya Naira 1000 wajen cikie bukatar sa ta neman aikin a yanar gizo, yayin da dama daga cikin masu neman aiki suka rasa rayukansu wajen tantancesu a shekarar da ta gabata.

Tsohon shugaban kamfanin Payfrorme Services Mista Augustine Ugorji tare da ma'aikaciyar Bankin Keystone Misis Bilkisu Mohammed, su ne masu bayar da shaidar na biyar da ta shida.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel