Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

A daren Laraba 4 ga watan Oktoba ne aka yi jana’izar tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, AVM Mukhtar Muhammad, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito an yi jana’izar AVM ne a jihar Kano, bayan da wani jirgin sama mai zamn kansa ya sauke gawarsa a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin karfe 7:35 na dare.

KU KARANTA: Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Jana'iza

Gawar mamacin ya samu rakiyar matarsa Hajiya Rabi, da kuma yayansa guda biyu Abba Mukhtar da Mukhtar Muhamamd, inda gawar ta samu tarba daga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Jana'izar

Saura mutanend a suka tari gawar mamacin su hada da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru Talamiz da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Jana'iza

Isowar gawar ke da wuya, motar daukan gawa ta rundunar Sojin sama ta dauki gawar zuwa kofar kudu na gidan Sarkin Kano, inda aka yi masa jana’iza tare da dubun dubatan jama’a suna yi masa addu’a.

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Iyalansa

Idan za’a tuna a ranar Lahadi ne AVM Mukhtar Muhammad ya rasu a wani asibiti a birnin Landan bayan wani gajeren jinya da yayi. Cikin wadanda suka halarci jana’izarsa akwai shugaban mayakan sojin sama Siddique Abubakar da sauran manyan mutane.

Hotunan sallar jana’izar AVM Mukhtar Muhammad, dubun dubatan mutane sun halarta

Jana'izar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Halin da ake ciki a kasuwannin Umuahia, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel