Mahajjata 16 da suka yi tattaki daga Kebbi zuwa jihar Niger don ganin rubutu larabci sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Mahajjata 16 da suka yi tattaki daga Kebbi zuwa jihar Niger don ganin rubutu larabci sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

- An rahoto cewa mutane 16 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

- Hatsarin jirgin ruwan ya afku ne a tsakanin jihohin Kebbi da Niger

- Hussaini Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar NSEMA ya tabbatar da al’amarin

Abun bakin ciki ya faru a safiyar ranar Talata tsakanin kauyukan Rofia da Mauta a Agwata dake karamar hukumar Borgu dake jihar Niger inda mutane 16 suka rasa rayukan su a hatsarin jirgin ruwa yayinda suke kokarin kallon rubutu larabci bisa wani dutse dake cikin tekun Niger.

Al’amarin ya auku ne yayinda jirgi mai dauke da fasinja 50 dake zuwa daga Zamare a jihar Kebbi ya kife bayan ya kara da wata bishiya.

An tattaro cewa gano gawawwaki 16, yayin da mutane biyu suka nutse sannan yan karkara da suka iya ruwa sun ceto sauran mutanen a raye.

Mahajjata 16 da suka yi tattaki daga Kebbi zuwa jihar Niger don ganin rubutu larabci sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Mahajjata 16 da suka yi tattaki daga Kebbi zuwa jihar Niger don ganin rubutu larabci sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Mai magana da yawun hukumar daake bada agaji cikin gaggawa a jihar Niger, Hussaini Abdullahi, a lokacin da aka tuntube shi, ya tabbatar da aukuwan al’amarin inda ya kara da cewa jirgin rowan ya bugi wata bishiya dake karkashin tekun ne sannan ya rabe biyu.

KU KARANTA KUMA: Buhari na kewaye da mutane dake jan kambun mulki domin ra’ayin kansu – Shehu Sani

Abdullahi ya ce hukumar ta tuntubi yan karkaran don samun bayanai kan adadin wadanda hatsarin ta shafa.

Ya kuma tabbatar da cewa fasinjojin sun fito ne daga jihar Kebbi don kallon rubutun larabci, wanda aka jingina ga annabi Muhammadu, a wata dutse dake cikin tekun River Niger.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel