Masu jefa kuri'a sun dawo daga rakiyar ku, PDP ta ce ma APC

Masu jefa kuri'a sun dawo daga rakiyar ku, PDP ta ce ma APC

- Wani Chiyaman na Jam'iyyar PDP reshen Jihar Oyo mai suna Tunde Akogun ya bayyana hakan

- Ya ce akwai yiwuwan ajam'iyyar ta su ta lashe zabe mai zuwa

- Ya kuma ce za su yi duk abin da ya kamata don dawo da martabar jam'iyyar ta su

Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa masu zabe sun dawo daga rakiyar Jam'iyyar APC. Chiyaman din kwamitin kulawa na PDP reshen Oyo mai suna Tunde Akogun ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Masu jefa kuri'a sun dawo daga rakiyar ku, PDP ta ce ma APC

Masu jefa kuri'a sun dawo daga rakiyar ku, PDP ta ce ma APC

Akogun ya sakankace akwai yiwuwan jam'iyyar ta su ta lashe zabe mai zuwa. Don haka ya dau alwashin yin duk abun da ya dace don dawo da martabar jam'iyyar ta su.

DUBA WANNAN: Tabbas doka zatayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

Sai dai kuma ya gardadi 'yan jam'iyyar da gudanar da taro ba bisa ka'ida ko samun izini ba. Ya ce za'a ladabtar da duk wanda aka kama laifin hakan.

Akogun ya kuma ce an tsayar da ranakun tarurruka na jam'iyyar a Jihar ta Oyo. An tsayar wa matakin shiyyoyi da kananan hukumomi ranakun asabar 21 da kuma 28 ga watan Oktoba. Sai kuma na matakin Jiha a ranar 4 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel