Buhari na kewaye da mutane dake jan kambun mulki domin ra’ayin kansu – Shehu Sani

Buhari na kewaye da mutane dake jan kambun mulki domin ra’ayin kansu – Shehu Sani

- Wasikar Dr Ibe Kachikwu ga shugaba Muhammadu Buhari da ya billon a cigaba da kawo cece-kuce a fadin kasar

- Ministan man fetur na jiha ya rubuta ma shugaban kasa wasika inda ya bukaci ya yi duba tare dashi kan zargin rashin da’a na shugaban kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC)

- Kachikwu ya zargi Manajan Darakta na kamfanin NNPC, Dr Maikanti Baru da kwangila da ya kai kimanin dala biliyan 26 ba tare da amincewar hukumar NNPC wanda Kachikwu ke shugabanta ba

Sanata mai wakiltan jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya maida martani ga wasikar da Dr Ibe Kachikwu ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sani wanda ya bayyana a shirin Chennels Television na Politics Today wanda aka shirya a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki sosai akan al’amarin da ministan jiha na man fetur ya gabatar.

Sanata Sani ya bayyana cewa idan ba’a binciki zarge-zarge ba, zai haifar da yanke hukunci mara dadi cewa an kwace ikon fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Nan da kwanaki 90 ku yi mana maganin fasa kauri – Hamid Ali ya bada oda

Ya kum ba yan Najeriya tabbacin cewa duk abunda shugaban kasar zai yi, majalisar dattawa bazata bari a rufe al’amarin ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kwamitin da majalisar dattawa ta kafa domin bincikar zargin zasu aiwatar da aiki mai inganci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel