Rikicin Baru da Kachikwu: Shugaba Buhari zai dauki matakin binciken NNPC

Rikicin Baru da Kachikwu: Shugaba Buhari zai dauki matakin binciken NNPC

- Mun fara jin cewa Shugaba Buhari zai dauki mataki game da rikicin Baru da Kachikwu

- Ministan mai na kasar ya kai karar Shugaban NNPC wajen Shugaban kasa Buhari

- Watakila za ayi bincike a Kamfanin NNPC bayan fasa kwan da Ministan fetur yayi

Mun fara jin kishin-kishin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dauki matakin binciken kamfanin man kasar na NNPC.

Rikicin Baru da Kachikwu: Shugaba Buhari zai dauki matakin binciken NNPC

Shugaba Buhari da Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu

Ku na da labari cewa Ministan man fetur na kasar Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya kai kukan cewa Dr. Mai Kanti Baru wanda shi ne Shugaban Kamfanin NNPC na kasa yana buga abin da ya ga dama a kanfanin man kasar.

KU KARANTA: Lauyan Nnamdi Kanu ya shiga uku

Yanzu haka za a zauna tsakanin Shugaban kasa Buhari da Shugaban NNPC Baru wanda aka zarga da bada ayyukan sama da Dala Biliyan $25 ba tare da bin ka’ida ba. Wani na kusa da fadar Shugaban kasar ne dai ya bayyana wannan.

Majiyar kuma ta bayyana cewa dai Shugaban kasar bai ji dadin abubuwan da ke cikin wasikar da Ministan na sa ya rubuta ba kwanaki inda ake tunanin zai dauki mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel