Nan da kwanaki 90 ku yi mana maganin fasa kauri – Hamid Ali ya bada oda

Nan da kwanaki 90 ku yi mana maganin fasa kauri – Hamid Ali ya bada oda

- Col. Hamid Ali ya bada wani oda ga Manyan Ma’aikatan Kwastam

- Shugaban Hukumar yace yana son ganin bayan fasa kauri a kasar

- A jiya ne dai Shugaban ya karawa wasu Jami’ai matsayi a Hukumar

Mun ji cewa Hukumar Kwastam ta bada lokaci domin ganin an yi maganin fasa kauri a kasar daga sababbin Jami’an da su ka samu karin matsayi zuwa matsayin DCG da ACG.

Nan da kwanaki 90 ku yi mana maganin fasa kauri – Hamid Ali ya bada oda

Shugaban kwastam na kasa Hamid Ali

Idan ba ku manta ba Hukumar kwastam na kasar ta karawa wasu Ma’aikatan ta matsayi zuwa Mataimakin kwanturola na DCG da ACG inda Shugaban Hukumar ya daura wani babban aiki a kan wuyan su bayan sun samu wannan girma.

KU KARANTA: Ministoci sun gagara ganin Shugaba Buhari

Shugaban Hukumar kwastam na kasa Kanal Hamid Ali mai ya fadawa wadanda aka karawa girma cewa su dage wajen ganin sun rage fasa kauri cikin nan da wata daya da rabi. Hamid Ali yace fasa kauri ya zama ala-ka-kai musamman wajen harkar shinkafa.

Hamid Ali mai ritaya ya kira wadanda aka karawa matsayin da su kare zage dantse wajen yi wa kasa aiki yace ko da dai yanzu Hukumar ta daga wajen nemawa kasa kudin shiga. Ali ya gargadi ma’aikatan da su tsaya su yi aiki yadda ya dace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel