Tataɓurza a majalisa: Majalisar dokokin jihar Kano ta ɓara dangane da sallamar Abdulmuminu da gaggawa

Tataɓurza a majalisa: Majalisar dokokin jihar Kano ta ɓara dangane da sallamar Abdulmuminu da gaggawa

Majalisar dokokin jihar Kano ta aika ma Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da doguwar takarda inda a ciki ta bayyana matsayarta dangane da dakatarwar da majalisar tayi ma Abdulmuminu JIbrin.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito majalisar jihar Kanon ta aike da wannan takarda ne a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba, inda ta bukaci Kaakaki ayi gaggawar mayar da wakilin al’ummar Kiru/Bebeji a majalisa Abdulmuminu.

KU KARANTA: Labara mai daɗi: Manoman shinkafa zasu karya farashinsa warwas!

Idan za’a tuna NAIJ.com ta ruwaito majalisar ta sallami Abdulmuminu Jibrin ne a lokacin daya fara tone tonen badakalar aringizon kasafin kudi, inda majalisar ta sallame shin a tsawon kwanaki 180.

Tataɓurza a majalisa: Majalisar dokokin jihar Kano ta ɓara dangane da sallamar Abdulmuminu da gaggawa

Abdulmuminu da Dogara

Sai dai a yayin zaman majalisar jihar Kano na ranar Laraba 4 ga watan Oktoba, dan majalisar jiha mai wakiltar KIru, Kabiru Dashi yace an hana ma al’ummar Kiru da Bebeji wakilci a majalisa har na tsawon shekara guda.

Don haka Dashi yace ya dace majalisar ta dawo da Jibrin, ganin cewa kwanakin da aka dibar masa na sallama sun cika, ko dan jama’an sa su cigaba da samun wakilci nagari.

Shima dan majalisa mai wakiltar Rano, Alhassan Rurum yayi amanna da batun Dashi, inda yace a mayar da Jibrin majalisar wakilai, sa’annan ya bukaci majalisar wakilan data matsa ma uwar jam’iyyar APC don ta sanya baki cikin lamarin.

Daga karshe sai majalisar ta amince da bukatar yayanta, inda Kaakakin majalisar Yusuf Ata ya umarci akawun majalisar daya aika ma Kaakakin majalisar wakilai takarda dake dauke da matsayar majalisar dangane da sallamar Abdulmuminu Jibrin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel