Sauran Lauyoyi sun yi kira a damke Lauyan Nnamdi Kanu

Sauran Lauyoyi sun yi kira a damke Lauyan Nnamdi Kanu

- Wasu Lauyoyi a kasar nan sun nemi a kama wanda yake kare Nnamdi Kanu

- Kungiyar wasu Lauyoyi tace Lauyan Kanu ke hura wutan rikicin Biyafra

- Wadannan Lauyoyi sun ce za su dauki mataki idan Gwamnati ta gaza

Labari ya kai gare mu cewa wasu Lauyoyi sun yi kira a damke Lauyan Nnamdi Kanu watau Barista Ifeanyi Ejiofor ba tare da bata lokaci ba.

Sauran Lauyoyi sun yi kira a damke Lauyan Nnamdi Kanu

Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu

Wasu Lauyoyin kasar nan a karkashin Kungiyar LAWCONS sun nemi a kama Lauyan da yake kare Jagoran Kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu mai suna Ifeanyi Ejiofor inda su kace rashin kunya ce ma har Lauyan ya shiga Kotun kasar yana nema a fito da Nnamdi Kanu bayan ya tsere.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun gargadi 'Yan ta'adda

Shugaban Kungiyar Babatunde Oladimeji ya bayyana wannan a Abuja yace Nnamdi Kanu ya saba dokar belin da ke kan sa kana kuma jama'ar sa sun kai hari ga Jami'an tsaro. Lauyan yace bai kamata Kotu ta kula karar ba tun da yanzu haka Kungiyar ta shiga cikin 'Yan ta'adda.

Oladimeji yace ba shakka tuni Nnamdi Kanu ya tsere zuwa Jihar Bayelsa tare da iyayen sa, daga nan ya shiga Kasar Kamaru wanda ta ke da alaka da Kasar Faransa da ake zargi da taimakawa Kungiyar ta IPOB.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel